3 Oktoba 2020 - 14:23
Kasashen Iran Da Rasha Sun Yi kira Da A Tsagaita Wutar Yaki A Yankin Nagorno-Karabakh

Ministocin hatrkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif da takwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, sun tattauna ta wayar tarho akan halin da ake ciki a yankin Nagorno-Karabakh a jiya Juma’a, tare da yin kira da a gaggauta tsagaita wutar yaki.

ABNA24 : Har ila yau, ministocin kasashen biyu sun yi kira ga dukkanin bangarorin Azerbaijan da Aremnia da su kaucewa yin maganganu da tsokana da za su kara ruruta wutar yaki.

Bugu da kari, kasashen na Iran da Rasha, sun bayyana cewa kasashen yanki da kuma makwabta za su iya taka rawa wajen samar da yanayin komawa kan teburin tattaunawa tsakanin Azerbaijan da kuma Armenia.

Kasashen Armenia da Azerbaijan sun koma yaki akan iyakokinsu a ranar Lahadi 27 ga watan Satumba, suna masu zargin juna da fara tsokana.

342/